Rarar farashin man fetur: Shugaba Buhari ya fadi abin da zayyi da kudaden da ya tara
- An sami karin farashin man fetura duniya
- shugaba Buhari ya ce ayyukan da basu bajat zayyi da kudaden
- Ziyarar shugaban kamfanin mai na ENI a Abuja
Ziyarar shugaban kamfanin mai na ENI a Abuja, fadar gwamnati, a yau dinnan, ta yi armashi. Ya sami tarba daga shuggaban kasa a fadar Aso Rock.
Farashin man fetur dai ya haura dala 70 a kan kowacce ganga, kuma Najeriya fitar da ganga miliyaan biyu a rana daya kullum.
A kasafin kudin bana kuwa, an sami banbancin kusan dala 30 a kan kowacce ganga. Wannan na nufin Najeroya na samun karin kudade da basu cikin kasafi miliyoyin daloli a kullum.
DUBA WANNAN: Amurka ta gindaya wa Najeriya sharudda kafin yaki da Boko Haram
Shugaba Buhari, a jawabinsa, ya bayyana cewa kudaden da ya tara daga wannan rarar, zai yi amfani dasu ne kan manyan ayyuka na raya kasa.
Kamar dai a zamanin mulkin soja, ya ce ayyukan tituna, jiragen kasa, da ma asibitoci irin na PTF, su za'a yi.
A jaawabin Mista Vella, shugaban kamfanin ENI na Italiya, ya ce kamfaninsa na hada gwiwa da na NNPC domin habaka matatun mai na kasar nan su kara yawan man fetur da ake tacewa a cikin gida, domin maye gurbin na waje da ake shigo da shi.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng