Sojin saman Najeriya sun nuna hotunan kayan aikin su na zamani, sun gwada mutane kyauta
- Sojin Saman Najeriya na zamanantar da ayyukanta a fannoni da dama
- A yau sunyi gwajin injinan kiwon lafiya da koyar da ma'aikatansu sarrafa su
- KAyan aikin sun hada da injinan hoto da scanning, an kwana biyar ana gwajin
Shafin acebook na sojin Najeriya, ya saki hotunan kayan aiki da gwaje-gwaje da suke yi wa mutane kyauta, da ma koyarwa ga ma'aikatansu.
Gwaje-gwajen sun shafe kwanaki biyar ana yi, da kayan aikin na zamani, wadanda suka hada da scanner, da x-ray machine, da MRI, duk na zamani.
DUBA WANNAN: Najeriya ta ki amincewa da sharuddan Amurka kan jirage
A kokarin su na mayar da ofishin da ofisoshinsu na zamani, hukumar NAF na ta sayen kayayyakin aiki, a fannoni da dama, na kiwon lafiya, da na sadarwa, gine-gine, da ma jirage, domin yaki da ta'addanci.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng