Abin da ka shuka shi zaka girba: Wani Likita zai kwashe shekaru 176 a gidan Yari saboda cin zarafin mata
Wani Likita a kasar Amurka, Larry Nassar ya gamu da fushin kotu, inda ta yanke masa hukuncin zaman gidan Yari na shekaru 176 a sakamakon kama shi da ta yi da laifin cin zarafin mata, musamman wadanda ke zuwa buda lafiyansu a wajensa.
Legit.ng ta ruwaito wannan hukunci ya biyo bayan zaman kwanaki shidda da kotun ta yi tana sauraran shaidu guda 160, dukkaninsu mata da iyaye, wadanda suka tabbatar da Likitan ya ci zarafinsu ta hanyar sanya hannunsa a gabansu, ko a mazauninsu, ko kuma ya matsa musu mama.
KU KARANTA: Rundunar mayaƙan Sojan ƙasa ta ƙaddamar da sabon aiki na musamman don yaki da barayin mutane
Da fari, Likitan ya musanta tuhume tuhumen, amma a ranar Laraba 24 ga watan Janairu sai yayi mi’ara koma baya, inda ya amsa laifinsa, yana cewa: “Ina rokon gafara daga gareku bias laifukan da na yi.”
Daga karsje mai shari’a Rosemarie Aquilina ta bada umarni a tasa keyarsa zuwa gidan kaso na jihar Michigan dake Amurka.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng