Kungiyar Gwamnonin Najeriya ta zargi NNPC da babakeren kudin al’ummar Najeriya
Kungiyar gwamnonin Najeriya ta zargi hukumar kula da albarkatun man fetir ta kasa, NNPC, da babakere tare da wawushe kudaden da aka tanadar don jin dadin yan Najeriya, inji rahoto Daily Trust.
Shugaban kungiyar, Abdul Aziz Yari ya bayyana ma shugaban kasa Muhammadu Buhari wannan a yayin wata ganawa da yayi da su a ranar Alhamis 25 ga watan Janairu a fadar Villa, inda yace NNPC ba ta shigar da dukkanin da suka dace zuwa susun bai daya..
KU KARANTA: Buhari ya gana da wasu gwamnoni a Aso Villa
Majiyar Legit.ng ta ruwaito Yari yana fadin kungiyarsu ta kafa kwamiti na mutum bakwai don ganawa da shuwagabannin hukumar inda suka tattauna da su kan matsalolin da suke ganin ake samu game da kudaden shiga da Najeryiya ke samu.
“Kwamitin mu ta samu tattaunawa da NNPC, don haka ne muka zo mu bayyana maka rashin jin dadin mu game da kudaden da hukumar ke bukata don gudanar da ayyukan, da kuma wanda take sanyawa cikin asusun hadin gwamnatin kasa.
“Mun lura cewa kudaden da suke bukata sun fi karfin kudaden da suka sanyawa cikin asusun gwamnati, don haka kungiyar mu ta damu kwarai da gaske, kuma muna ganin akwai lauje cikin nadi, suna cutar da Najeriya gaba daya.” Inji Yari.
Gwamna Yari ya bayyana cewa daya daga cikin hujjojin da hukumar ta baiwa gwamnonin shi ne cewa tun daga shekarar 2010 a lokacin da farashin gangan mai yake a kan dala 110, ba’a taba neman a bada kudaden aiki ga hukumar ba, har zuwa shekarar 2015.
“Don haka dalilin da yasa asusun gwamnatin tarayya ke kara yin kasa shi ne saboda suna biyan kudaden aiki a yanzu, sa’annan suna biyan na baya da ba’a biya ba, don haka muka nemi hanyar shawo kan lamarin, musamman yadda farashin mai ke cigaba da karuwa.” Inji shi.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng