Sayen jiragen yaki: Sabuwar takaddama ta shiga tsakanin Najeriya da kasar Amurka

Sayen jiragen yaki: Sabuwar takaddama ta shiga tsakanin Najeriya da kasar Amurka

Da alama dai dangantaka ta so tayi tsami bayan da kasar Najeriya ta sanar da kin amincewar ta game da wasu sharudda da kasar Amurka ta gindaya mata bisa kudurin ta na sayen jiragen yaki daga kasar ta kamar dai yadda ministan tsaro, Mansur Dan-Ali ya sanar.

Mun samu dai cewa minista Mansur Dan-Ali dai ya bayyana cewa majalisar zartaswar kasar nan a baya ta amince da kudi zunzurutu da suka kai $494 miliyan domin sayen jiragen yakin a baya.

Sayen jiragen yaki: Sabuwar takaddama ta shiga tsakanin Najeriya da kasar Amurka
Sayen jiragen yaki: Sabuwar takaddama ta shiga tsakanin Najeriya da kasar Amurka

KU KARANTA: Ganduje ya bayar da filin da za'a gina sabon gidan kurkuku

Legit.ng haka zalika ta tsinkayi ministan yana cigaba da cewa amma sai kuma daga bisani sharuddan da kasar ta gindaya wa Najeriya ba za'a iya amincewa da su ba musamman ma na cewa sai a shekarar 2020 ne za su sayar da jiragen.

A wani labarin kuma, Akalla 'yan Najeriya kimanin mutane miliyan 50 ne masu sana'ar saye-da- sayarwar tireda ne a karkashin inuwar kungiyar National Harmonised Traders Union, a turance suna sanar da ba shugaban kasar Najeriya dukkanin cikakken goyon baya a zaben 2019 mai zuwa.

Shugaban kungiyar ne dai kamar yadda muka samu bayani daga majiyar mu mai suna Dakta Bature Abdulaziz ya sanar da hakan a yayin wani taron manema labarai da ya shirya a garin Kano dake arewa maso yammacin Najeriya.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng