Dutse: An garkame masu safarar miyagun kwayoyi 14 a Jigawa

Dutse: An garkame masu safarar miyagun kwayoyi 14 a Jigawa

- Hukumar ‘yan sandan jihar Jigawa ta cafke wasu mutane 14 da ake zargi masu safarar miyagun kwayoyi ne a jigawa

- Hukumar ta ce jami’an 'yan sandan sun kai hari ne a wuraren da ake zato wadannan mutane ke boyewa

- Mai magana da yawun hukumar ya ce an saki 7 daga cikin wadanda ake tuhuma bayan an gano ba masu laifi bane

Rundunar ‘yan sanda reshen jihar Jigawa ta kama wasu mutane goma sha huɗu da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi bayan da jami’an tsaro suka kai musu hari a wuraren uku da ake zato suna boyewa a yankin karamar hukumar Dutse na jihar.

SP Abdu Jinjiri, mai magana da yawun 'yan sanda a jihar, ya tabbatar da kama wadannan mutane ga NAN majiyar Legit.ng a Dutse ranar Alhamis, 25 ga watan Janairu.

A cewar Jinjiri, jami’an 'yan sandan sun kai hari ne a Yantifa, Three Star Junction da kuma Gindin Dinya wuraren da ake zato wadannan mutane ke boyewa.

Dutse: An garkame masu sarrafa miyagun kwayoyi 14 a Jigawa
‘Yan sandan Najeriya

Ya ce, "An kai hare-haren ne a ranar Alhamis a misali karfe 4:00 na rana bayan da muka samu bayanan sirri a kan ayyukan wadanda ake tuhuma”.

KU KARANTA: Hukumar Sojin Kafa ta damke mutane 11 saboda bacewar wani soja

Jinjiri ya ce, an saki bakwai daga cikin wadanda ake tuhuma bayan an gano ba masu laifi bane yayin da za a gurfanar da wasu a gaban kotu a lokacin da aka kammala bincike a kan batun.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng