Ganduje ya ba da filin da za a kaura da gidan kurkuku da ke tsakiyar Kano
- Gwamnatin Kano ta ba da fili a Janguza inda za a kaura da gidan kurkuku da ke tsakiyar Kano
- Gwamnan jihar ya ce an riga an biya diyya ga masu mallakar filayen a yankin
- Shugaban hukumar ya bukaci gwamnatin jihar ta taimaka musu da motocin aiki
Gwamnatin jihar Kano ta samar da wata fili a Janguza a bayan birnin Kano, inda ake shirin kaura da gidan kurkuku da ke tsakiyar garin Kano wanda ke Kurmawa kwata.
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, wanda ya bayyana hakan a lokacin da ya karbi bakuncin sabon shugaban hukumar gidajen kurkuku, Alhaji Magaji Ahmed Abdullahi a lokacin ziyararsa, ya ce an riga an biya diyya ga masu mallakar filayen a yankin.
Kamar yadda Legit.ng ke da labari , Ganduje ya ce wannan aikin ya kasance ne bayan gwamnatin jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin tarayya don kaura da tsohon gidan Kurkuku da ke Kurmawa.
Gwamnan ya ce gwamnatin jihar, daidai da umarnin shugaban kasa game da gyare-gyaren gidajen kurkuku, ta biya nauyin kudi ga wasu fursunoni masu kananan laifuka, don tallafa a saki su, tare da cewa an kammala shiri wanda zai taimaka wajen sake saki wasu 'yan fursunonin wadanda suka cancanta a fadin jihar.
KU KARANTA: Gwamnatin tarayya za ta baiwa 'yan Najeriya 8m kulawar lafiya kyauta a 2018
A jawabinsa, shugaban hukumar, Alhaji Magaji Ahmed Abdullahi ya bukaci gwamnatin jihar ta taimaka wa hukumar da motocin aiki da kuma kyamarori a gidajen kurkuku, don taimaka musu wajen magance matsalolin da suke fuskanta.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng