Antoni Janar na kasa ya aike wa da EFCC kashedin kada su kama Adoke kan Malabu

Antoni Janar na kasa ya aike wa da EFCC kashedin kada su kama Adoke kan Malabu

- Badakalar malabu, ta ki ci taki cinye wa

- Kar ku sake ku kama Adoke, don hujjarku bata da kwari, inji Malami ga Adoke

- Dala biliyan daya aka sace a lokacin cinikin rijiyar man ta Malabu OML245

Antoni Janar na kasa ya aike wa da EFCC kashedin kada su kama Adoke kan Malabu
Antoni Janar na kasa ya aike wa da EFCC kashedin kada su kama Adoke kan Malabu

Ministan shari’a na Najeriya, Abubakar Malami, ya bukaci hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC), da ta sake duba wadanda ake tuhuma da laifi akan badakalar mai na Malabu.

Mutanen da ake zargi sun hada tsohon ministan man fetur, Dan Etete, tsohon ministan shari’a, Mohammed Adoke, da sauran wadanda ake tuhuma da zargin cin hanci da rashawa na man fetur na dala biliyan daya.

DUBA WANNAN: An ware wa makiyaya wurin kiwo a Katsina

Hukumar ta EFCC ta na tuhumar su da karkatar da kudi adadi mai yawan gaske, na man fetur. Mista Malami ya fitar da zargin nasu ne a wata sanarwa da aka bashi a kotu ranar Alhamis din nan, daga hannun mai bada shawara na Mista Adoke.

A bayanin da muka samu Mista Malami yace shaidar da ake da ita akan wadanda ake tuhumar bata bada tabbacin cewar sun aikata laifin ba.

A cewar shi, Mista Kanu Agabi, ya bukaci kotun tarayya dake Abuja akan ta bada umarnin janye duk wata tuhuma da ake yi wa Mista Adoke din, saboda ana tuhumar sa ba bisa ka’ida ba. Kuma yabi umarnin tsohon shugaban kasa ne wato Goodluck Jonathan.

Ya kara da cewar, shaidar takardun da aka bayar a kotu ita ce take nuna cewar bashi da hannu a cikin wannan badakalar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng