Hukumar NNPC tayi aman Naira 135.14 biliyan zuwa ga asusun gwamnatin tarayya
A majallar kwana-kwanan nan da hukumar rukunin kamfunnan albarkatun man fetur ta kasa watau Nigerian National Petroleum Corporation, NNPC ta fitar ta bayyana cewa ta zuba kimanin akalla Naira 135.14 biliyan a cikin asusun gwamnatin tarayya a cikin shekarar 2017.
Hukumar dai ta bayyana hakan ne a cikin mujallar da ta saki a jiya Laraba inda ta bayyana cewa kamfanin ya sayar da danyen man da ya kai $239 miliyan a cikin watan Nuwamnar bara.
Legit.ng dai ta samu cewa wannan bayanin da rukunin kamfanin na nuni da cewa yanzu an fara samun daidaituwar al'amurra a wurin musamman ma ganin yadda a baya cin hanci da rashawa suka yi katutu a bangaren.
A wani labarin kuma, Wata kotun daukaka kara mallakin gwamnatin tarayya dake zaman ta a garin Abuja ta sha alwashin sai ta garkame tsohon kakakin jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) a takaice watau Olisa Metuh idan dai har bai gurfana a gaban ta ba ranar 5 ga watan Fabrairun shekarar nan.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
Asali: Legit.ng