Yanzu-Yanzu: Hukumar zabe ta INEC ta sanar da lokacin rufe yin rijisar katin zabe
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa watau Independent National Electoral Commission, INEC a turance ta sanar da cewa zata rufe yin rijistar masu yankan katin zabe na kasa a cikin watan Disemba mai zuwa.
Hukumar a don haka ne ma ta bukaci dukkan wanda yasan bai da katin kuma yana bukatar yayi zabe a shekara ta 2019 da ya hanzarta ya yi rijistar domin samun dama.
KU KARANTA: Buhari ya shiga ganawa da gwamnoni
Legit.ng ta samu cewa haka zalika hukumar ta sanar da cewa ta tsara za'a cigaba da bude ofisoshin yin rijistar ga dukkan mai sha'awa daga karfe 9 na safe zuwa karfe 3 na yammacin ko wace rana ciki kuwa hadda ranakun hutu.
A wani labarin kuma, Hukumar nan ta jami'an tsaron farar hula ta kasa watau Nigeria Security and Civil Defence Corps NSCDC, reshen jihar Neja a takaice ta bayyana samun nasarar cafke akalla litocin main fetur 469,000 a garin Mokwa ana kokarin haurawa da su kasar Benin.
Kamar dai yadda shugaban rundunar mai suna Yakubu Ayuba ya bayyanawa manema labarai a garin Minna, litocin man na cikin wasu manyan motoci ne mallakin wani babban dan kasuwa.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
Asali: Legit.ng