Hukumar NSCDC ta kama litar man fetur 469,000 ana kokarin haurawa da su Benin

Hukumar NSCDC ta kama litar man fetur 469,000 ana kokarin haurawa da su Benin

Hukumar nan ta jami'an tsaron farar hula ta kasa watau Nigeria Security and Civil Defence Corps NSCDC, reshen jihar Neja a takaice ta bayyana samun nasarar cafke akalla litocin main fetur 469,000 a garin Mokwa ana kokarin haurawa da su kasar Benin.

Kamar dai yadda shugaban rundunar mai suna Yakubu Ayuba ya bayyanawa manema labarai a garin Minna, litocin man na cikin wasu manyan motoci ne mallakin wani babban dan kasuwa.

Legit.ng dai ta samu cewa kasar ta Najeriya na fama da matsanancin karancin man fetur tun karshen shekarar da ta gabata.

Hukumar NSCDC ta kama litar man fetur 469,000 ana kokarin haurawa da su Benin
Hukumar NSCDC ta kama litar man fetur 469,000 ana kokarin haurawa da su Benin

KU KARANTA: Wasu kungiyoyi a Najeriya za su kauracewa cin naman shanu

A wani labarin kuma, A majallar kwana-kwanan nan da hukumar rukunin kamfunnan albarkatun man fetur ta kasa watau Nigerian National Petroleum Corporation, NNPC ta fitar ta bayyana cewa ta zuba kimanin akalla Naira 135.14 biliyan a cikin asusun gwamnatin tarayya a cikin shekarar 2017.

Hukumar dai ta bayyana hakan ne a cikin mujallar da ta saki a jiya Laraba inda ta bayyana cewa kamfanin ya sayar da danyen man da ya kai $239 miliyan a cikin watan Nuwamnar bara.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng