Yanzu-Yanzu: An rufe filin jirgin Abuja saboda wani jirgi ya samu tagardar sauka

Yanzu-Yanzu: An rufe filin jirgin Abuja saboda wani jirgi ya samu tagardar sauka

Labarin da muke samu yanzu-yanzu na nuni da cewa an rufe filin sauka da kuma tashin jiragen sama na kasa-da-kasa na tunawa da Nnamdi Azikwe dake a garin Abuja.

Mun samu dai cewa an rufe filin jirgin ne na dan wani lokaci biyo bayan wata 'yar tangarda da wani jirin yawo mallakin kamfanin Nest Oil ya samu yayin da yake kokarin sauka a yau din nan.

Yanzu-Yanzu: An rufe filin jirgin Abuja saboda wani jirgi ya samu tagardar sauka
Yanzu-Yanzu: An rufe filin jirgin Abuja saboda wani jirgi ya samu tagardar sauka

KU KARANTA: Tsohon minista ya sha alwashin takawa Fayose birki

Legit.ng ta samu cewa wannan sanarwar dai ta fito ne daga bakin karamin ministan sufuri na kasa dake kula da harkokin jiragen sama watau Sanata Hadi Sirika a cikin wani sako da ya saki a kafar sadarwar zamani ta Tuwita.

A wani labarin kuma, Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari a yau din nan ranar Alhamis, 25 ga watan Janairun shekara ta 2018 ya gana da shugabannin jami'an tsaron kasar a yunkuri da ake kallo kamar na dakushe tabarbarewa tsaron da ake fama da shi a ofishin sa dake a Abuja.

Mun samu dai cewa babban ministan tsaron kasar Mansur Dan-Ali ne dai tare da taimakon babban mai ba shugaban kasar shawara ta fannin tsaro Babagana Monguno suka yi wa jami'an tsaron jagora a taron.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Asali: Legit.ng

Online view pixel