Kwamitin tsaro ya datsi wasu makiyaya a jihar Delta
A kwana-kwanan nan ne, wata rundunar tsaro akan makiyaya da manoma da ta ƙunshi jami'an 'yan sanda na jihar Delta, ta yi arangama da wasu makiyaya da shanun su na kiwo a jihar.
Kakakin rundunar, DSP Andrew Aniamaka, shine ya bayyana hakan a wata sanarwar ranar Alhamis a birnin Asaba, inda ya bayyana cewa makiyaya sun furucin shigowa jihar ne daga jihar Kogi.
Andrew yake cewa, rundunar da shiga fagen daga ne a sakamakon yaduwar wani bidiyo a dandalan sada zumunta da ya bayyanar da wasu makiyaya da suka tsallako tekun Neja zuwa birnin Asaba riƙe da makamai.
KARANTA KUMA: Tsagerun Neja Delta sun jeranto wasu muhimman kadarorin man fetur da zasu hallakar
Legit.ng ta fahimci cewa, a sakamakon wannan rahoto ne rundunar ta bazama cikin aikin lalube, kuma tayi nasarar yin kacibus da wannan makiyaya, inda jagoran rundunar, Cif Cassidy, wanda babban hadimin gwamnan jihar ne ya titsiye makiyayan da tambayoyi.
Kakakin rundunar ya bayyana cewa, daga bisani an maishe da wannan makiyaya zuwa jihar su ta Kogi, domin babu ku guda da aka riska da wani makami.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng