Obasanjo zai kafa kungiya don tsige Buhari daga mulki

Obasanjo zai kafa kungiya don tsige Buhari daga mulki

Rahotanni sun kawo cewa tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo na hadahada don ganin ya tsige shugaban kasa Muhammadu Buhari daga mulki a shekarar 2019 ta ko wani hali.

Tuni dai tsohon shugaban kasar ya fara jan hankulan yan siyasa domin sun mara masa baya akan wannan kudiri nasa wanda ya sha banban da manufofin PDP da APC.

Obasanjo yace jam’iyyun APC da PDP duk watangaririya kawai suke yi.

Alamomin Obasanjo ya fara gajiya da salon takun mulkin Buhari, wanda shi Obasanjo din ya mara wa baya a zaben 2015, sun fara fitowa fili ne tun bayan da ya aika wata wasika ga shugaba Buhari, inda ya shawarce shi da kada ma ya yi gingin sake takara a zabe mai zuwa.

Obasanjo zai kafa kungiya don tsige Buhari daga mulki
Obasanjo zai kafa kungiya don tsige Buhari daga mulki

Haka zalika kafin wannan wasika tsohon shugaban kasar yayi hannunka mai sanda ga shugaba Buhari a wani taro day a hallata a jami’ar Oxford.

KU KARANTA KUMA: Hukumar NDLEA sun kama sojan bogi, sun samo alburusai da kayan sojoji

Inda Obasanjo ya yabi yadda wasu shugabannin Afrika suka farfado da tattalin arzikin kasashen su, amma sai bai yi maganar Najeriya ba.

Sai dai kuma a lokacin da aka tambaye shi abin da zai ce dangane da Najeriya, sai Obasanjo ya ce ai lokacin da zai yi magana kan Najeriya bai yi ba tukunna.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng