Hukumar NSCDC ta damke tankokin mai 8 dauke litan mai 469,000 da za’a karkatar jamhuriyyar Benin
Kamfanin man feturin Najeriya, NNPC, ta bayyana cewa jami’an hukumar yan sandan farar hula wato Nigeria Security and Civil Defence Corps (NSCDC) shiyar jihar Neja sun damke tankokin man fetur 8 cike da man fetur lita 469,000 a Mokwa, jihar Neja.
Kakakin Kamfanin NNPC Mr. Ndu Ughamadu, wanda ya saki wannan jawabi ya ce an damke tankokin ne a Babana, iyakan Najeriya da Benin.
Jawabin ya bayyana cewa shida daga cikin tankokin na mutum daya ne.
Kana ya bayyana cewa sauran tankoki biyun na dauke da litan 132,000 sabanin lita 66,000 da ya kamata.
KU KARANTA: Tsagerun Neja Delta sun jeranto wasu muhimman kadarorin man fetur da zasu hallakar
Ya jaddada cewa wajibi ne masu tankoki suyi bayani akan inda tankokin zasuje kuma idan aka tabbatar da cewa karkatar da mai za’ayi, za’a ci su tarar N200 akan kowani lita daya.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a: https://facebook.com/naijcomhausa https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng