Ruguntsumi: Wuf Trump ya kashe 'yan ISIL 150 a taronsu na Siriya

Ruguntsumi: Wuf Trump ya kashe 'yan ISIL 150 a taronsu na Siriya

- An ragargaji mayakan ISIL a Iraki da Siriya

- Sun sulale zuwa Pakistan da Najeriya da Afghanistan

- Harin jirgi ya kashe mayakan 150

Ruguntsumi: Wuf Trump ya kashe 'yan ISIL 150 a taronsu na Siriya
Ruguntsumi: Wuf Trump ya kashe 'yan ISIL 150 a taronsu na Siriya

A ranar Asabar ne jiragen yakin Amurka suka yi ruwan wuta kan mayakan ISIL wadanda suka taru a kasar Syriya, domin shirin kai hare-hare, bama-bamai suka yi musu lugude. A cewar ma'aikatar tsaron Amurka ta Pentagon kuma, harin yayi nasarar hallaka mayakan kungiyar har 150.

Mayakan sun hallara ne bayan da aka tarwatsa su daga garin Deir-Az-Zour, na Siriyar, sai dai makamai masu linzami sun isar musu bayan da bayanan sirri suka nuna maboyarsu.

DUBA WANNAN: Benue: Da saura kan lamarin tsaro

Rundunar sojin hadaka da Amurka ke jagoranta ta ce kungiyar IS ta yi asarar kashi 98 cikin 100 na yankinta da ta kwace daga Iraki da Syria a 2014, a lokacin da ta yi ikirarin kafa daular musulunci.

A yanzu yankin da IS ke iko da shi ba shi da wani girma a Siriya, inda ya hada da wani bangare na tsaunin Euphrates, wanda rundunar sojin hadaka da Amurka ke jagoranta ta kai wa hari.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng