An cafke wani matashi da ake zargi ya sace bindiga a Enugu
- An damke wani saurayi mai shekaru 22 da laifin sace bindiga a Enugu
- Wanda ake tuhuma yana fuskantar zargin laifuka guda biyu a kan sata da fashi, da kuma sace N400,000
- Alkalin kotun tace za a ci tarar masu shaidu da aka ambata a cikin lamarin idan basu bayyana a kotu ba
Kotun Majistare ta Enugu a ranar Laraba, 24 ga watan Janairu ta tura keyar wani mai suna Onyebuchi Nwatu, mai shekaru 22 da haihuwa a kurkuku saboda zargin cewa ya yi satar bindiga.
Kamar yadda Legit.ng ke da labari, Nwatu na fuskantar zargin laifuka guda biyu a kan sata da fashi, da kuma sace dubu dari hudu na wani mutum mai suna Linus Ugwu.
Lauya wanda ya gabatar da kara, Mista Chima Nwachwukwu ya shaida wa kotun cewa wanda ake tuhuma ya aikata laifukan a ranar 21 ga Disamba, 2017 a garin Ndiolo da ke karamar hukumar Nchatancha, Emene a jihar Enugu da ke kudu maso gabashin kasar.
Mai gabatar da kara ya ce bindigar ta kasance malakar ƙungiyar tsaro na ‘yan banda da ke yankin.
KU KARANTA: An yi musayar wuta da asarar rai tsakanin 'yan sandan Najeriya da wasu 'yan fashi da makami
Alkalin kotun, Misis C.R. Nwoye ta bayyana cewa kotun ba ta da hurumin sauraren karar ko ba shi beli.
Nwoye ta ce shaidu da aka ambata a cikin lamarin zasu biya kudi naira dubu dari idan basu bayyana a kotu ba.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng