Cutar zazzabin bera: Gwamnati ta sanya dokar hana shan Garin-Kwaki
Gwamnatin jihar Anambra, ta sanya dokar ta baci don hana shan garin kwaki a dukkanin fadin jihar, sakamakon bincike da ya nuna danyen Garin kwaki na kawo cutar zazzabin beraye.
Gwamnan jihar, Willie Maduabuchukwu Obiano ya tabbatar da wannan haramci, biyo bayan bincike da hukumar lafiya ta Duniya, WHO ta yi, wanda ya nuna cewar cutar zazzabin Lassa na yaduwa ta hanyar abincin da fitsarin bera ya taba.
KU KARANTA: Akalla sahihan Malamai 45,000 makarantun jihar Kaduna su ke bukata – Inji Malam Nasiru
BBC Hausa ta ruwaito Garin kwaki a matsayin wani nau’in abinci da ake samar da shi daga Rogo, kuma a kan ci shi ne ta hanyar shan shi danye da ruwa da siga, ko kuma a tuka shi ya zama Teba, yan kabilar Ibo ne suka fi cin wannan abinci.
Sai dai wannan haramci bai shafi Teba ba, tunda bincike ya nuna muddin aka dafa Garri, har aka tuka shi, toh tabbas an kasha duk wasu kwayoyin cutar zazzabin beraye, wato Lassa dake dauke a cikin Garri.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito Kwamishinan lafiya na jihar Anambra, Dakta Joe Akabuike yace “Irin garin da ake shanyawa a kan titi don ya bushe,kafin a kai shi kasuwa, na da illa sosai, don haka shan sa na tattare da hadari.”
A yan kwanakin nan ana ta yawan samun Karin yaduwar cutar zazzabin Lassa a fadin Najeriya, musamman yankin kudu maso kudancin Najeriya da kuma yankin kudu maso gabashin kasar.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng