Kudirin dakatar da mutanen da Buhari ya turo mana mu tantance yana nan - Saraki
- Majalissar dattawa ta yanke hukuncin dakatar da tanatance mutanen da Buhari ya turo musu saboda kalaman da Osinabajo yayi akan Ibrahim Magu
- Akwai mutane guda 50 da majalissa dattawa ta ki tantancewa da Buhari ya turo musu
Shugaban majalissar dattawa, Dakta Bukola Saraki, ya ce Kudirin majalissar na dakatar da tantance mutanen da Buhari ya turo musu yana nan.
Saraki ya mayar da martani ne akan jawabin da Sanata Mao Ohuabunwa (PDP, Abia) akan kudirin kirkiro hukumar bunkasa yankin Neja Delta (NDDC), inda Saraki yace za su ba duka kudirori fa’aida majalissar.
A watan Yuni na shekara da ta gabata majalissar dattawa ta zartar da hukuncin dakatar da duka mutanen da Buhari turo su tanatance.
KU KARANTA : Fayose yayi kaca-kaca da Obasanjo akan budaddiyar wasikar da ya rubutawa Buhari
Majalissar ta yanke wannan hukuncin ne saboda kalaman da mataimakin shugaban kasa, Ferfesa Yemi Osinbajo yayi dangane da mukaddashin shugaban hukumar EFCC Ibrahim Magu.
Wannan kudiri ya shafi mutaen guda 50 da shugaban kasa ya tura a tantance su akan mukamai daban-daban.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng