Buhunhunan shinkafa 1,150 jami'an hukumar Kwastam su ka kama a Kano da Jigawa

Buhunhunan shinkafa 1,150 jami'an hukumar Kwastam su ka kama a Kano da Jigawa

- Jami'an hukumar Kwastam rukunin "B" sun ce sun kama buhunhunan shinkafa 1,150 a jihohin Kano da Jigawa

- Shugaban rundunar jami'an kwastam na rukunin "B", Alhaji Usman Dakingari, ya sanar da hakan a Kano

- Ya ce jami'an hukumar sunyi nasarar kama shinkafar ne bayan samun bayanan sirri

Shugaban hukumar hana fasa kwabri ta kasa, da aka fi sani da Kwastam, rukunin "B", Alhaji Usman Dakingari, ya sanar da cewar jami'an dake aiki karkashin rukunin da yake jagoranta sun yi nasarar kama fiye da buhunhunan shinkafar kasar waje dubu daya da aka shigo da su jihar Kano ta barauniyar hanya.

Dakingari ya bayyana haka ne yayin da yake nuna shinkafar da su ka kwace ga manema labarai a jiya, a garin Kano.

Buhunhunan shinkafa 1,150 jami'an hukumar Kwastam su ka kama a Kano da Jigawa
Buhunhunan shinkafa 1,150 jami'an hukumar Kwastam su ka kama a Kano da Jigawa

Ya bayyana cewar jami'an hukumar sun yi nasarar kama shinkafar ne bayan samun bayanan sirri da suka tabbatar da boye buhunhunan shinkafar a wani gida dake unguwar Dakata a cikin birnin Kano.

DUBA WANNAN: Gwamna Tambuwal ya kaddamar da fara sayar da takin gargajiya da aka sarrafa a jihar Sokoto

Kazalika, Dakingari ya ce sun yi nasarar kama wata mota makare da buhunhunan shinkafar ta kasar waje jihar Jigawa.

Bayan buhunhunan shinkafar, hukumar ta ce ta kwace wasu kayan gwanjo masu yawa da aka shigo da su.

Dakingari ya jaddada aniyar hukumar Kwastam na dakile aiyukan fasa kwabri. (NAN)

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng