Sojoji da ‘yan sanda sun fi kamuwa da Kanjamau a Najeriya - NACA
- Hukumar NACA ta bayyana mutanen da suke fi kamuwa da cutar kanjamu a Najeriya
- Dakta Aliyu ya ce jami'an sojoji da 'yansanda sun fi kowa kamuwa da cutar kanjamau a Najeriya
Shugaban hukumar hana yaduwar kwayar cutar kanjamau a Najeriya (NACA), Dakta Sani Aliyu, yace binckiken da hukumar ‘kula da halin zaman jama’a da yanayi’ ta gudnar ya nuna cewa jami'an sojoji da ‘yan sanda suna cikin kungiyoyi shida da suka fi kowa kamuwa da cutar kanjamau a Najeriya.
Dakta Sani Aliyu, ya bayyana haka ne a wata taro da jami’an tsaro suka shirya a birnin Abuja.
Yace bincken da aka gudanar ya nuna jami’an tsaro 220,000 suka kamu da cutar kanjamau a cikin shekara 2017 a Najeriya.
KU KARANTA : 2019: Jam’iyyar APC har ta fadi zabe mai zuwa inji wani babban Lauya
Daga karshe Aliyu ya ce, binciken ya nuna direbobi da kwandastoci sune ke biye da ‘yansanda da sojoji wajen kamuwa da wannan cuta, sai kuma karuwai dake luwadi.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng