Dangote zai iya tsamo mutane miliyan 2 daga kangin talauci – Kungiyar Oxfam
Hasashe da kungiyar Oxfam ta yi ya nuna cewa kudin ruwan da mai kudin Afrika, Alhaji Aliko Dangote ke samu zai iya tsamo mutane kimanin miliyan biyu daga cikin kangi na talauci.
Kungiyar ta yi ikirarin cewa tazarar dake tsakanin attajirai da talaka ya karu a wannan shekarar.
Kungiyar ta kuma jaddada cewa mutane 42 da suka kasance biloniya sun samu makudan kudade kimanin dala biliyan 3.6 a duniya.
Har ila yau kungiyar ta ce kashi daya cikin dari na attajiran duniya ne suke tafiyar kaso 82 cikin dari na dukiyar dake fadin duniya.
Oxfam ta ce abin da ya kara taimakawa manyan attajiran wajen tara dimbin dukiyar shi ne yadda wadansu daga cikinsu suke kauce wa biyan kudaden haraji.
KU KARANTA KUMA: Wani Babban Dan APC ya nemi Buhari ya hakura da maganar tazarce
Har ila yau akwai kuma batun yadda suke amfani da gwamnatoci wajen yin dokoki da za su ci gajiyarsu, a cewar kungiyar.
Sai dai masana a fannin hada-hadar kudi sun sanya alamar tambaya game da wadansu daga cikin abubuwan da kungiyar take ikirari.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng