Jami’a za ta hukunta duk ɗalibin da ya zazzago da wandonsa, da masu askin banza
Hukumar Jami’ar Ilori dake jihar Kwara ta haramta ma dalibai mata sanya Karin gashi, da kuma fent fenten fuska, cikin wata sanarwar data fitar a ranar Litinin 22 ga watan Janairu, ini rahoton The Cable.
Su ma maza, an haramta musu zazzago da wandonsu kasa, da kuma kitse kansu, sa’annan sanarwar ta kara da cewa duk dalibin da aka kama ya karya doka, toh doka za tayi aiki a kansa.
KU KARANTA: 2019: Abubuwan da Obasanjo ya gaya wa shugaba Buhari a wasikarsa don kar yayi takara
“An haramta ma dalibaimata sanya gajerun siket, matsatstsun wanduna, kaya masu shara shara, Karin gashi da sauransu, Maza kuwa an haramta musu zazzago da wando, yagaggun wanduna, gajerun wanduna da askin banza.” Inji sanarwar.
Sanarwa ta kara da cewa ba’a yarda dalibiya karya dokokin nan ba a cikin makaranta ko kuma wuraren da suka hada da dakin jarabawa, azuzuwa, dakin karatu, dakin gwaje gwajen kimiyya. Daga karshe hukumar ta bukaci kowanne dalibi ya daura shaida dalibtarsa a wuya.
Legit.ng ta ruwaito ana samun matsalar shigar banza a tsakanin daliban jami'o'in Najeriya da sauran manyan makarantun gaba da sakandari, wanda hakan na taimaka wajen gurbata tarbiyyar yara da dama.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng