Mabambantan ra'ayoyi na cigaba da kwaranya game da wasikar Obasanjo zuwa ga Buhari

Mabambantan ra'ayoyi na cigaba da kwaranya game da wasikar Obasanjo zuwa ga Buhari

Kawo yanzu dai ra'ayoyi daban-daman mabanbanta na ta cigaba da kwaranya daga bakunan 'yan Najeriya tun bayan da tsohon shugaban kasar Najeriya Janar Olusegun Obasanjo ya rubutawa shugaba Buhari wasikar kin goyon baya game da sake tsayawar sa takara a 2019.

Shi dai daya daga cikin jiga-jigan jam'iyyar Cif Bola Tinubu da mu jam'iyyar ta APC duka sun fada cewa zai bayar da na shi martanin idan ya kammala nazarin wasikar.

Mabambantan ra'ayoyi na cigaba da kwaranya game da wasikar Obasanjo zuwa ga Buhari
Mabambantan ra'ayoyi na cigaba da kwaranya game da wasikar Obasanjo zuwa ga Buhari
Asali: Twitter

KU KARANTA: Tsaffin sojoji 5 da 'yan sanda za su ba Kwankwaso kariya a Kano

NAJI.com ta samu cewa shi kuwa tsohon shugaban jam'iyyar APGA mai suna Dakta Victor Oye cewa yayi tsohon shugaban bai da hurumin da zai yi irin wannan maganar.

Ita kuma jam'iyyar PDP a matsayin ta na babbar jam'iyyar adawa, ta bayyana cewa tabbas tsohon shugaban kasar ya kara tabbatar da abunda ta dade tana fadawa 'yan Najeriyar ne.

A wani labarin kuma, Ciyaman din kwamitin majalisar dattijan Najeriya dake sa ido game da harkokin babban birnin tarayya, Abuja watau Sanata Dino Melaye daga jihar Kogi a jiya ya zargi hukumar nan dake kula da rukunin albarkatun man fetur na kasa watau NNPC da wata sabuwar badakala.

Sanatan dai ya zargin hukumar ce ta Nigerian National Petroleum Corporation (NNPC) a turance da budewa tare da yin anfanin da wani haramtaccen asusun adana kudi na dalar amurka da yanzu haka ke dauke da akalla $ 137 miliyan.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng