Wata sabuwa: Makiyaya sun hallaka Hausawa biyu sanadiyyar rikici daya ɓarke kan Rake
Wani rikici daya balle a kan Rake a kasuwar ruwa guri dake garin kan iyakar Najeriya da Nijar yayi sanadiyyar mutuwar mutum biyu Hausawa a hannun yan Fulani makiyaya.
Gidan rediyon muryar Amurka ta ruwaito rikicin ya samo asali ne a lokacin da wani bahillace ya siya rake a hannun wani Bahaushe mai rake, amma da Bahaushe ya tambaye shi kudi, sai bahillacen yayi biris da shi, ya ki biyansa, kamar yadda shugaban Yan bangan gari Ruwa Wuri Umaru Ahmad ya bayyana.
KU KARANTA: Tsohon gwamna ya bayyana dalilin ziyarar da suka ka ma Buhari yau a Villa
Majiyar Legit.ng ta ruwaito hana mai rake kudinsa da Fulani yayi ne ya harzuka mai raken, inda shi kuma bahillace ya zaro wukarsa ya caka ma mai rake, kafin ka Ankara kasuwa ta dauka ana ta dauki ba dadi tsakanin yan kabilun biyu.
Umar ya tabbatar da mutuwar mutum 2, dukkaninsu Hausawa, daa suka hada da Burgawu, da kuma wani matashi dan gidan Marin garin.
Hakimin garin, Alhaji Usman ya bayyana cewa bayan aukuwa lamarin, sun gayyaci shuwagabannin kungiyar Miyetti Allah, da na Hausawa inda aka tattauna tare da fahimtar juna don gudun sake faruwar hakan a gaba.
A nasa jawabin ga majiyar Legit.ng, wani jigo a kungiyar Miyetti Allah, Usman Shehu Bature,ya tabbatar da a cewa a yanzu an yi sulhu, kuma zaman lafiya ya dawo kasuwar, don a yanzu kowa na cigaba da hidimar gabansa.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng