Gwamnatin Ribas na zargin gwamnatin Buhari da wai son yafewa masu kungiyar sihiri da aka kama
- Gwamnatin Tarayya tana kokarin yiwa wasu ‘yan kungiyar asiri afuwa
- An sha samunn hare-hare da kashe-kashe a yankunan jhar daga kungiyoyin masu tsafi
- Ana tsama dama tsakanin jihar ta PDP da gwamnatin Tarayya ta APC
Gwamnatin jihar Rivers tace ta gano wani yunkuri da gwamnatin tarayya take nayin afuwa ga wasu yan kungiyar asiri guda 32, wanda ita gwamnatin jihar ta bada umarnin a kamo su.
Gwamnatin jihar tace ta samu wannan rahoton ne daga wasu bayanan sirri, inda suka tabbatar mata cewar gwamnatin tarayya din tana so tayi masu afuwan ne saboda tana so tayi amfani dasu wurin kamfen din zabe mai zuwa na 2019.
Kwamishinan yada labarai na jihar, Emma Okah, yayi jawabi ga manema labarai, jiya a garin fatakwal. Ya zargi gwamnatin tarayya akan neman gurbata harkar tsaro a jihar.
Ya kara da cewa gwamnatin jihar ta samu tabbacin cewar, gwamnatin tarayya ta gama duk wasu shirye-shiryen ta na ganin ta cimma manufar ta na yiwa ‘yan kungiyar asirin afuwa. A bayanan da muka samu mun gano cewar gwamnatin tarayya tana so tayi amfani da wadannan mutane ne saboda ta samu nasara a zabe mai zuwa.
"Wannan mataki da gwamnatin tarayya ta dauka bai bamu mamaki ba, saboda mun sha fada cewar akwai wadanda suke da hannu a cikin jami’ai da hukumomin gwamnatin tarayya, akan rikice-rikicen da suke faruwa a jihar rivers. Sannan muna zargin (SARS) da hannu wurin aikata ta’addanci a jihar mu."
DUBA WANNAN: An soki Buhari kan 'son kai' ga makiyaya
Yayi kira ga al’umma dasu sanya ido akan abinda yake faruwa na ganin an bata duk wani kokari da jihar take yi akan harkar tsaro. Don kaucewa shakku, gwamnatin jihar rivers zata cigaba da aiki da jami’an tsaro don tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a a jihar.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng