Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Sanata Shehu Sani ya gargadi George Weah, daga daukar shawarwari da yin koyi da jagoranci da kuma kaucewa yawaita ziyara a Najeriya. An rantsar da George Weah a ranar Litinin da ta gabata a matsayin sabon shugaban kasar Laberiya.

Sanata Shehu Sani ya shawarci sabon shugaban kasar Laberiya, George Weah, cewa kada ya kuskura ya yi amfani da shawarwari da jagorancin kasar Najeriya a mulkinsa. Sanatan ya kuma bukaci shugaban ya kaucewa yawaita ziyara a Najeriya.

Sani, sanata wanda ke wakiltar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawan Najeriya ya bukaci Weah ya yi koyi da wasu abubuwan Najeriya a matsayinta na kasa , kuma ya jagoranci Laberiya zuwa nan gaba.

Legit.ng ta tattaro cewa, Sani a cikin wasikar shi zuwa ga sabon shugaban wanda ya wallafa a shafinsa ta Twitter ya ce: “Masoyi Weah, kada ka dauki shawarwarinmu, kada ka yi koyi da shugabancinmu, kada ka ziyarci nan akai-akai, kada kuma ka yarda da yawan ziyara, ka yi koyi da irin abubuwan da muke fama da su, kuma ka jagoranci al'ummarka zuwa nan gaba”.

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya
Sanata Shehu Sani

KU KARANTA: Wata tsaleliyar Budurwa ta saki hotunan dalleliyar motar da tace Shehu Sani ya yi mata kyauta

Idan dai baku manta ba Weah, mai shekaru 51 da haihuwa, a ranar Litinin da ta gabata ne ya karbi ragamar mulki daga tsohuwar shugaban kasar, Ellen Johnson Sirleaf, wanda ta kwashi shekaru 12 tana mulkin kasar bayan yakin basasa.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel