Darajar Naira ta karu a kan Dala da Yuro a kasuwar hada-hadar kudade

Darajar Naira ta karu a kan Dala da Yuro a kasuwar hada-hadar kudade

- Naira ta samu karin daraja a kan kudin Dala ta Yuro a kasuwar hada-hadar kudade

- Ana musayar Naira a kan N364 kowacce Dala, N500 a kan Fam na Ingila, da N440 a kan kowanne Yuro

- Ana alakanta darajar ta Naira da kudin da babban bankin kasa ya ingiza a kasuwar hada-hadar kudade

Kudin Naira ya samu tagomashi a kasuwar hada-hadar kudade ta kasa bayan babban bankin kasa ya ingiza Dala miliyan $210 domin saukakawa jama'a.

Binciken Legit.ng ya tabbatar da cewar Naira ta samu karin daraja da yayin da ake sayar da ita a kan N364 kowacce Dala (N364/$1).

Darajar Naira ta karu a kan Dala da Yuro a kasuwar hada-hadar kudade
Darajar Naira ta karu a kan Dala da Yuro a kasuwar hada-hadar kudade

Farashin Fam din Ingila a kan N500 da Yuro a kan N440. Ana ganin darajar Naira ta karu ne saboda ingiza Dalar Amurka miliyan $210 domin saukakawa jama'a.

KU KARANTA: Bala Lau ya zama shugaban kungiyar Izala ta nahiyar Turai

Wani mai rikon kwaryar mukamin darekta a bankin, Mista Isaac Okorafor, a wata sanarwa da bankin ya fitar a jiya Litinin, 22 ga watan Janairu, ya ce bankin zai cigaba da bayar da agaji domin Naira ta cigaba da samun tagomashi.

Ya ce CBN ta bayar da dala miliyan $100 ga wasu 'yan kasuwar canjin kudi masu rijista da bankin yayin da kananun 'yan kasuwar canjin su ka samu Dalar Amurka miliyan $55.

Okorafor ya jaddada aniyar babban bankin na cigaba da bayar da tallafin dalar Amurka ga 'yan kasuwar ta canji domin samun habakar harkokin kasuwanci.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng