Wata tsaleliyar Budurwa ta saki hotunan dalleliyar motar da tace Shehu Sani ya yi mata kyauta
- Sanata Shehu Sani bai mayar da martani ko hakan gaskiya bane
- An ruwaito cewa Sanatan yaka ce wal=bani-wal baka
- Budurwar ta ce shi ya yi mata kyautar
- An san Sanata Shehu Sani da kyauta
Sanata Shehu Sani mai wakiltar Kaduna ta tsakiya mutum ne mai farin jini wurin jama'a, musamman ma 'yan mata, don haka ba abub mamaki bane idan wata tace yayi mata kyauta, domin abun hannunshi baya tsone masa ido.
Sai dai masu sharhi a soshiyar midiya na tantamar kalaman budurwar da ta wallafa a shafinta cewa sanatan yayi mata kyautar mota, inda wata jarida wallafa, mai suna MIKIYA, ta kuma ce ai dama ya kan ce wal-bani wal-baka...
DUBA WANNAN: Yan PDP na ci gaba da yabawa matar Buhari
Budurwa mai suna Maryam Hassan, ta wallafa a shafinta na facebook cewa sai dai magabta su mutu, domin Sanata Shehu Sani yayi mata kyautar mota, ta miliyoyin kudi, kamar dai tana yi wa wasu kawayenta ne habaici da martani.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng