Kwantena cike da kayan sojoji da makamai ya bace a tashar ruwan Apapa

Kwantena cike da kayan sojoji da makamai ya bace a tashar ruwan Apapa

- Jami'an 'yansanda da na Kwastom sun shiga cikin rudani yayin da Kwantena cike da kakin soja da makamai ya bace a tashar ruwan Apapa dake jihar Legas

- Kwamishinan ‘yansanda dake kula da tashoshin ruwan Legas yaba runduar ‘yansadar jihar Legas sa’o’i 24 su nemo kwatenan da ta bace

Wata kwatena da aka shigo da ita Najeriya cike da kakin soja da makamai ya bace a tashar ruwan Apapa dake jihar Legas.

A ranar Litinin kwamishinana ‘yansanda dake kula da tashoshin ruwan Legas, Celestine Okoye, yaba runduar ‘yansadar jihar sa’o’i 24 su nemo kwatenan da ya bace tare da kama wadanda suka shigo da kwantenan.

Al’amarin bacewar kwantenan ya saka jami’an ‘yansanda da na kwastom cikin rudani, saboda kashe-kashen da ake ta yi a fadin kasar wanda ake zargin makiyaya ke yi.

Kwantena cike da kakin soja da makamai ya bace a tashar ruwan Apapa
Kwantena cike da kakin soja da makamai ya bace a tashar ruwan Apapa

Legit.ng ta samu rahoton cewa, kwantenan ya shigo Najeriya ne a ranar Juma’a kuma duk kokarin da jami’an ‘yansanda suka yi na ganin cewa kwantenan ba wuce ba, sai da aka bari ya wuce.

KU KARANTA : Kungiyar CAN ta kirkiri rikicin makiyaya - JNI

Rahotanni sun nuna cewa kafin kwantena ya barce sai da jami’an ‘yansanda suka sanar da kwamishina 'yasanda, daganan yaba da umarni kada a kuskura a bar kwantenan ta wuce

Amma m’aikatan tashar ruwan sunce sai da kwantena ta wuce kafin suka samu umarnin dakatar da ita.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng