Labari mai dadi: Matatar mai ta saman ruwa zata iso Najeriya yau

Labari mai dadi: Matatar mai ta saman ruwa zata iso Najeriya yau

Labarin da muke samu daga majiyoyin mu na nuni ne da cewa a yau ne ake sa ran isowar wata matatar mai ta samn ruwa mai yawo da ka iya tace gangar danyen mai dubu dari biyu a kowace rana watau dai Floating Production Storage Offloading (FPSO) vessel a turance.

Mun samu dai cewa matatar man an kiyasar kudin ta da suka kai $3.3 biliyan kuma ta taho ne daga kasar Koriya ta kudu inda aka kera ta kimanin watanni uku da suka gabata.

Labari mai dadi: Matatar mai ta saman ruwa zata iso Najeriya yau
Labari mai dadi: Matatar mai ta saman ruwa zata iso Najeriya yau

Legit.ng ta samu dai cewa idan har matatar man ta iso gabar tekun Najeriya, ana sa ran za'a cigaba da aikin kammala hada ta da wasu rijiyoyin mai mallakin kasar dake a cikin teku kafin daga bisani ta fara aiki gadan-gadan .

Haka zalika mun samu cewa ana sa ran zuwan na wannan matatar man zai kawo karshen wahalar man da kasar ke fama da shi a wasu lokunan.

A wani labarin kuma, Mun samu labarin cewa zanga-zangar kin jinin gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta gudana a birnin Landan dake can a kasar Ingila jiya litinin a wani salo don jawo hankalin mutanen duniya.

Mun samu dai cewa al'ummar kabilar Tiv ne dake zaune a kasar ta Ingila suka gudanar da zanga-zangar da nufin nuna rashin jin dadin su ga yadda rikicin fulani da makiyaya ke cigaba da jawo salwantar rayuka da dukiyoyin 'yan uwan su a nan gida Najeriya.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng