Jami'an 'yan sanda sun cafke wani da yayi wa abokiyar aikin su bugun-kawo-wuka

Jami'an 'yan sanda sun cafke wani da yayi wa abokiyar aikin su bugun-kawo-wuka

Jami'an 'yan sandan Najeriya dake a garin Legas a ofishin 'yan sandan garin Itire sun sanar da samun nasarar cafke wani matashi mai suna Samson Aghedo bisa zargin sa da suke yi da lakadawa abokiyar aikin su bugun tsiya.

Labaran da muka samu dai sun bayyana cewa 'yar sandan dai ta je ta kamo mutumin ne a gidan sa dake a kan titin Ola mai lamba 32 saboda wani laifin da ya aikata amma sai ya hauta da bugu daga bisani.

Jami'an 'yan sanda sun cafke wani da yayi wa abokiyar aikin su bugun-kawo-wuka
Jami'an 'yan sanda sun cafke wani da yayi wa abokiyar aikin su bugun-kawo-wuka

Legit.ng dai ta samu cewa tun farko dai mutumin ya nuna tirjiya tare da kin amincewa da kamen da 'yar sandan ta zo ta yi masa wanda yayi sanadiyyar cece-kuce da cacar baki tsakanin su kafin daga bisani ya tura ta kasa ya kuma hau ta da duka.

A wani labarin kuma, Wata kotun al'ada dake a karamar hukumar Ikole-Ekiti a can jihar Ekiti a jiya Litinin ta sanar da saka ranar 5 ga watan Fabreru na wannan shekarar domin yanke hukunci ga wani mutum da da ya bukaci a raba auren sa da matar sa saboda ta bar gida kimanin kwanaki 11.

Sai dai bayan sauraron karar da ya shigar alkaliyar kotun mai suna Yemisi Ojo ta sanar da cewa a wannan ranar zata yanke hukuncin.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng