Wani ya dirkawa mahaukaciya ciki a jihar Bauchi, har ta haihu

Wani ya dirkawa mahaukaciya ciki a jihar Bauchi, har ta haihu

Tabbas inda ranka, za ka cigaba da ji da kuma ganin abubuwan al'ajabi a duniya kamar dai yadda muka samu cewa an samu wani maras imani da yayi wa wata mahaukaciya ciki a jihar Bauchi dake a arewa maso gabashin Najeriya.

Mun samu dai cewa wannan abun takaicin ya faru ne a karamar hukumar Shira dake a jihar ta Bauchi kuma yanzu haka ma dai har mahaukaciyar ta samu ta haihu lafiya a kwanakin baya.

Wani ya dirkawa mahaukaciya ciki a jihar Bauchi, har ta haihu
Wani ya dirkawa mahaukaciya ciki a jihar Bauchi, har ta haihu

Legit.ng ta samu dai cewa ita dai mahaukaciyar wadda ake yi wa lakani da 'Boka' amma mai suna Lami na gaskiya ta bayyana cewa wani mutum ne daga wani kauye dake kusa da su yayi mata cikin.

A wani labarin kuma, Jami'an 'yan sandan Najeriya dake a garin Legas a ofishin 'yan sandan garin Itire sun sanar da samun nasarar cafke wani matashi mai suna Samson Aghedo bisa zargin sa da suke yi da lakadawa abokiyar aikin su bugun tsiya.

Labaran da muka samu dai sun bayyana cewa 'yar sandan dai ta je ta kamo mutumin ne a gidan sa dake a kan titin Ola mai lamba 32 saboda wani laifin da ya aikata amma sai ya hauta da bugu daga bisani.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng