Rushe ofishin jam'iyyar PDP a Maiduguri ya bar baya da kura
- An rushe ofishin jam'iyyar PDP a Maiduguri
- Jam'iyyar PDP ta zargi gwamnatin jihar Borno da muzguna ma ta
- An zargi ofishin da zama matattarar masu shaye-shaye
Jam'iyyar PDP a jihar Borno ta zargi jam'iyyar APC mai mulki da muzgunawa magoya bayanta ta hanyar amfani da karfin iko.
Zargin na jam'iyyar PDP na zuwa ne bayan gwamnan jihar, Kashim Shettima, ya bayar da umarnin rushe tsohon ginin Prime Cinema, daya daga cikin fitattun gine-gine a garin Maiduguri.
Ginin dake kan hanyar zuwa fadar Shehun Borno, ya taba zama shelkwatar tsohuwar jam'iyyar ANPP tsakanin 1999 zuwa 2015.
Saidai ginin ya kasance kango tun bayan yin maja. Dalilin da hukumar NDLEA ta ce wurin ya zama dandalin sha da sayar da mugayen kwayoyi da ragowar kayan maye.
Saidai rushe ginin ranar Lahadi da hukumar raya birnin Maiduguri ta yi ya jawo cece-kuce.
DUBA WANNAN: Yadda wani kudirin majalisar dattijai ke kokarin jawo mata takun saka da fadar shugaban kasa
Jim kadan bayan rushe ginin, jam'iyyar PDP a jihar ta bayyana cewar da gan-gan gwamnatin jihar ta rushe ginin saboda jin labarin ta kama hayar wurin a matsayin shelkwatar ta ta jihar.
Wani jigo a jam'iyyar PDP a jihar Borno, Baba Isa, ya shaidawa manema labarai cewar kafin rushe ginin, saida gwamnatin jihar ta matsawa masu wurin su janye hayar da suka bawa jam'iyyar PDP.
Kakakin jam'iyyar APC a jihar, Makinta Zarami, ya musanta wannan zargi na jam'iyyar PDP a zantawar sa manema labarai.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng