Rikcin Makiyaya : Ina zargin wasu ‘yan siyasa da daukan nauyin ta'adancin dan bata sunan Fulani -Oladimeji Odeyemi
- Kwamared Oladimeji Odeyemi ya ce za a iya kawo karshen rikicin makiyaya da manaoma a Najeriya inda aka daina siyasantar da al'amarin
- Oladimeji ya ce yana zargin wasu 'yan siyasa da daukan nauiyn bata sunan al'umman Fulani
Kwamared Oladimeji Odeyemi, jagoran kungiyoyin dake fafutika da yaki ta’adanci a Najeriya (COCSAT) ya tofa albarkacin bakin sa akan kashe-kashen da ake zargin makiyaya Fulani da yi.
Da aka tambaye shi akan yanayin tsaro a kasar, Oladimeji Odeyemi yace shugaban kasa, Muhammadu Buhari, mutum ne da yayi alkawarin kare rayuka da dukiyoyin al’umma Najeriya kuma yana iya kokarin sa a wannan fannin.
Oladimeji Odeyemi ya jajantawa mutanen jihar Benuwe akan kashe masu ‘yan uwa da abokan arziki da aka yi.
Odeyemi, ya ce akwai rashin gaskiya dangane da kashe-kashen da ake zargin makiyaya Fulani suna yi s kasar. "Ina da tabbacin cewa akwai wasu ‘yan siyasa dake yunkirn bata sunan kabilan Fulani a fadin kasar.
KU KARANTA : ‘Yan Najeriya miliyan 7.5m ne basu da aiki yi tun daga shekara 2016 - Hukumar NBS
“Ni bayarabe ne amma bazan taba barin wani ya danganta duka ‘yan kabila na da ta’adanci ba.
A lokacin da ake ta cecekuce akan kashe-kashen da ake zargin makiyaya Fulani sun yi, kada mutane su manta suma Fulanin an ka kashe musu 'yan uwa a jihar Taraba, Katsina ,Zamfara da Birnin Gwari a Kaduna tare da sace shanu.
Oladimeji ya ce, matakin farko na magance matsalar makiyaya da manoma a kasar shine a daina siyasantar da al’amarin, mataki na biyu kuma shine inganta fannin tsaro a kasar.
Ya kuma shawarci ‘yan Najeriya da su yi amfani da damar babban zaben da za gudanar a 2019 su zabi shugabanni masu adalci.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng