Dutse: Gobarar wuta ta halaka yara 4 ‘yan gida daya a Jigawa
- Gobarar wuta ta yi sanadiyar mutuwar yara 4 ‘yan gida daya a Jigawa
- Kakakin hukumar tsaro ta sibil difens ya bayyana cewa ƙyallen wuta daga na'urar lantarki ya haifar da gobarar
- Kakakin ya ce lamarin ya faru ne a garin Hadeja a ranar 20 ga Janairu a misalin karfe 10:45 na dare
Wani mumunar gobarar wuta ta kashe wasu tagwaye uku tare da ɗan'uwansu a garin Hadejia da ke jihar Jigawa.
Mai magana da yawun hukumar tsaro ta sibil difens reshen jihar Jigawa, Mista Adamu Shehu, a ranar Litinin, 22 ga watan Janairu ya bayyana hakan.
Shehu ya bayyana cewa ƙyallen wuta daga na'urar lantarki ya haifar da wannan mumunar gobarar wutar.
Ya ba da sunayen tagwayen uku a matsayin, “Hassan Sale, Hussain Sale da Muhusin Sale masu shekaru biyar da haihuwa da kuma ɗan'uwansu, Aliyu Sale mai shekaru 2, dukkanin su iyali daya”.
KU KARANTA: Wuta ta cinye shaguna 50 da kwantenan kifi 30 a Kano
Ya ce wannan lamarin ya faru ne a gidan Alhaji Sale Tela na Tudun Tanda a garin Hadeja a ranar 20 ga Janairu a misalin karfe 10:45 na dare.
Kakakin ya shawarci jama'a su yi taka tsantsan yayin da suke amfani da kayan lantarki, musamman a lokacin hunturu saboda kaucewa gobarar wuta.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng