Rikicin Makiyaya: ‘Yan bindiga sun kashe mutane 3 a kauyen Numan

Rikicin Makiyaya: ‘Yan bindiga sun kashe mutane 3 a kauyen Numan

Wasu 'yan bindiga da ba a sani ba sun kai hari a kan wani kauyen Numan da ke jihar Adamawa a ranar Lahadi da ta gabata, inda suka kashe mutane uku da kuma kone gidajensu. ‘Yan bindigar sun kai wannan harin ne a misali karfe 2 na safe.

Wasu 'yan bindiga da ba a tantance ba sun kashe mutane uku a yankin karamar hukumar Numan da ke jihar Adamawa. Mazaunan garin Kikan sun shaida wa majiyar Legit.ng cewa, sun gano gawawwakin 'yan uwansu uku ne bayan harin da ake zaton makiyaya ne suka kai a kauyen.

Legit.ng ta tattaro cewa, ‘yan bindigar sun kai harin ne a misali karfe 2 na safe, inda suka ta harbe-harbe da kuma kone gidaje.

Rikicin da ta ki cinyewa tun lokacin da aka kashe makiyaya 55 ciki har da yara da mata a watan Nuwamban da ta shude da kuma hare-haren da aka kai a kan al’umman Bachama inda aka kashe mutane da dama.

Rikicin Makiyaya: ‘Yan bindiga sun kashe mutane 3 a kauyen Numan
‘Yan bindiga
Asali: Depositphotos

Mazaunan yankin sun ce 'yan bindigar sun shigo kauyen ne zaman babura a cikin dare lokacin da suke barci, suka fara kone gidajensu da kuma harbi ga wasu mutane da suke kokarin gudu zuwa daji don kare rayukansu, inda suka kashe mutane uku.

KU KARANTA: Hukumar DSS ta yi ikirarin gano mambobin ISIS a jihar Benue, Kogi da Edo

Euphraimu Paul Turaki, wani dan gwagwarmaya a yankin kuma shugaban matasa a Numan, ya yi baƙin ciki game da asarar rayukan mutane marasa laifi a harin ranar Lahadi da kuma tilasta wasu gudun hijira daga gidajensu, yana kira ga hukumomi su tashi tsaye wajen samar da tsaro da kuma kare rayukan al’umman yankin a matsayinsu na 'yan ƙasa.

Kakakin 'yan sanda a jihar Adamawa, SP Othman Abubakar, ya ce tuni hukumar ta tura' yan sandan Mobiles zuwa yankin don samar da tsaro da kuma kama 'yan bindigar.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng