Dandalin Kannywood: Sarki Ali Nuhu ya bayyana gaskiyar alakar sa da Yarima Adam A. Zango

Dandalin Kannywood: Sarki Ali Nuhu ya bayyana gaskiyar alakar sa da Yarima Adam A. Zango

Ko shakka babu fitattun jaruman nan na wasannin fina-finan Hausa a masana'antar Kannywood watau Ali Nuhu da kuma Adam A. Zango sun zama bangaye abun jingina ga dukkan masu sha'awar kallon na fim din wasa.

To sai dai a lokuta da dama rade-rade na yawo na cewa jaruman basu jituwa da junan su ko kadan musamman ma ganin cewa suna zaune ne a garuruwa daban daban.

Dandalin Kannywood: Sarki Ali Nuhu ya bayyana gaskiyar alakar sa da Yarima Adam A. Zango
Dandalin Kannywood: Sarki Ali Nuhu ya bayyana gaskiyar alakar sa da Yarima Adam A. Zango

Hakan ya sanya Jarumi Ali Nuhu din ya fito ya bayyanawa duniya irin hakikanin alakar dake tsakanin sa da abokin sana'ar ta sa yayin wata fira da yayi da majiyar mu a kwanakin baya.

Ali Nuhu din dai wanda ake kira da Sarki a masana'antar ta Kannywood ya bayyana cewa akwai alaka mai karfi tare da girmamawa a tsakanin shi da Adam A. Zano din wadda ya kamata ta da irin ta 'yan uwantaka.

Ali Nuhu din ya kuma bayyana cewa su kan dade basu hadu ba amma da zarar sun hadu shike nan za su cigaba da harkokin su a tare tamkar dai 'yan uwan.

Haka nan kuma jarumin ya bayyana cewa shi bai san dalilin da ya sa ake kiran sa Sarki ba shi kuma Adam A. Zango Yarima.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng