Kamar Benue: Gwamnatin jihar Taraba za ta kaddamar da dokar hana kiwo

Kamar Benue: Gwamnatin jihar Taraba za ta kaddamar da dokar hana kiwo

Gwamnatin jihar Taraba dake a yankin Arewa maso gabashin kasar nan ta bayar da tabbacin cewa ita ma za ta bi sahun jihar Binuwai wajen kaddamar da dokar da zata haramta kiwo a jihar.

Kwamishinan shari'a ne dai na jihar ya bayyana hakan inda ya kara da cewa bin matakin kafa dokar ya zama dole ganin yadda gwamnatin tarayya ta kasa daukar matakin da ya dace wajen cafko wadanda suka kai harin Binuwai.

Kamar Benue: Gwamnatin jihar Taraba za ta kaddamar da dokar hana kiwo
Kamar Benue: Gwamnatin jihar Taraba za ta kaddamar da dokar hana kiwo

KU KARANTA: An kama gwamnan Benue da hannu cikin rikicin jihar sa

Legit.ng ta samu cewa a wani labarin kuma, Gwamnatin jihar Bauchi dake a Arewa maso gabashin Najeriya ta yi fatali da rade-raden da ake ta yawo da su na cewa tana shirya makarkashiyar korar ma'aikatan ta a 'yan kwanakin nan.

Shugaban ma'aikatan gwamnati na jihar Alhaji Liman Bello shine ya sanar da hakan yayin da yake tattaunawa da 'yan jarida a ofishin sa karshen satin da ya gabata.

Alhaji Liman Bello dai ya bayyana cewa maganar korar ta ma'aikata a jihar labarin kanzon kurege ne kawai da bai da tushe balle makama da acewar sa wasu da basu kaunar gwamnatin suna yada wa.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng