Jonathan ya fi kowa talauci a cikin tsaffin shugabannin kasar Najeriya
Wani tsohon jakadan Najeriya kuma fitaccen dan siyasa mai suna Ambassador Godknows Igali ya bayyana tsohon shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan a matsayin wanda yafi kowa talauci a cikin tsaffin shugabannin kasar Najeriya.
Ambassador Godknows Igali dai yayi wannan ikirarin ne yayin da yake wata tattaunawa da manema labarai a gidan sa inda ya bayyana cewa har yanzu ana bin shugaban basussuka da dama.
KU KARANTA: Jam'iyyu 19 na shirin dunkulewa donzaben 2019
Legit.ng ta samu haka zalika cewa Ambassador Godknows Igali ya kara da cewa duk da yadda ya rika shan suka daga kowane bangare na kasar nan, Jonathan a yanzu ya tabbata daya daga cikin manyan mutanen da duniya take alfahari da su.
A wani labarin kuma, Yanzu haka labaran da muke samu daga majiyoyin mu na nuni ne da cewa akalla jam'iyyu sha tara ne ke shirin dunkulewa wajen guda domin kalubalantar manyan jam'iyyun da ke garemu yanzu a Najeriya na APC da kuma PDP.
Wannan dai kamar yadda muka samu daga jagoran shirin dunkulewar kuma shugaban daya daga cikin jam'iyyun watau Freedom and Justice Party (FJP), mai suna Dakta Onwubuya Breakforth inda yace tuni shire-shire sun yi nisa.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
Asali: Legit.ng