Kungiyar CAN ta kirkiri rikicin makiyaya - JNI

Kungiyar CAN ta kirkiri rikicin makiyaya - JNI

- Kungiyar CAN ta zargi gwamnatin Buhari da yiwa Kristocin Najeriya kisan ‘kare dangi

- Jamatul Nasir Islam (JNI) ta zargi kungiyar Kristoci Najeriya CAN da kirkiran rikicin makiyaya

Kungiyar Musulman Najeriya, Jamatul Nasir Islam (JNI) ta zargi kungiyar Kristoci Najeriya CAN da kirkiran rikicin makiyaya.

Da yake jawabi a taron manema labarai a ranar Lahadi a Kaduna , sakataren kungiyar JNI, Dakta Khalid Aliyu, ya maida martani ga wani jawabi da sakataren Kungiyar CAN Dr. Musa Asake yayi kwanakin baya inda ya zargi Gwamnatin Shugaba Buhari da yi wa Kiristocin Najeriya kisan ‘kare dangi.

Khalid Aliyu yace karya kungiyar CAN ta ke yi kuma dole a bayyana gaskiya, ba don kare gwamnati ba sai dai don kare Musulmai daga sharrin da ake yi masu.

Kungiyar CAN ta kirkiri rikicin makiyaya - JNI
Kungiyar CAN ta kirkiri rikicin makiyaya - JNI

JNI tace ba ta manta da lokacin da wani Fasto (Johnson Suleman)yayi kira da a kashe Fulani a kasar nan ba.

KU KARANTA : Aisha Buhari mace ce mai basira - Ben Bruce

Bayan haka Dr.Khalid yace akwai lokutan da aka rika kama Kiritoci a lokacin da suke kokarin kona coci da sunan Musulmai a Najeriya amma CAN tayi shiru ba ta ce komai ba.

A Jihar Benuwe an kama masu ta’adanci kuma babu musulmi ko makiyayi guda daya a cikin su.

An kashe musulmai da yawa a jihar Taraba, Kaduna, Zamfara, da Katsina amma Kristoci sun yi shiru basu ce komai ba.

Duk da kashe-kashen da akayi jihar Ribas CAN ta ki yin magana amma ta juya hankalin ta akan rikcin da ya auku a jihar Kwara da sauran su.

Kungiyar ta JNI ta gargadi fastocin kasar akan furta kalaman batanci da zai iya janyo rikici da cigaba da raba kawunan al’ummar kasar.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng