Sanatan Najeriya ya fusata, ya yi gargadi da babbar murya ga 'yan uwansa Sanatoci
- Sanata Abdullahi Adamu ya nuna fushinsa a kan kalaman da wasu Sanatoci ke yi ga shugaban kasa Buhari
- Sanatan ya ce akwai hanyoyin da mambobin za su iya bayyana ra'ayi ko fushinsu ba tare da kalaman jagaliyancin siyasa ba
- Sanata Adamu ya bayyana haka ne yayin mahawara a kan batun rikicin makiyaya da manoma
Sanatan Najeriya kuma tsohon gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Adamu, ya harzuka yayin da 'yan majalisar dattijai ke gudanar da mahawara a kan rikicin makiyaya da manoma.
A wani faifan bidiyo da Legit.nghausa ta ci karo da shi, an ga Sanata Adamu cikin kakkausar murya yana gargadi ga mambobin majalisar da su guji yin kalaman jagaliyancin siyasa ga shugaba Buhari ko gwamnatin sa.
DUBA WANNAN: Dubi hotunan amarya yayin da ta Haukace ana tsaka da shagalin bikinta, har ma yayyaga kayan amarcinta
"Ko kadan bai dace ba muke amfani da kalaman jagaliyancin ba yayin bayyana ra'ayin mu ko bayar da shawara ba. Ba dai-dai ba ne muke aibata shugaba Buhari ba saboda an samu barkewar rikici a wasu jihohi ba", inji Sanata Adamu.
Adamu ya fito baro-baro ya shaidawa 'yan majalisar cewar majalisar ba za ta yarda da cin fuskar shugaba Buhari ko gwamnatinsa ba.
Sanata ya zargi abokan aikin na sa da amfani da mahawara a kan rikicin makiyaya da manoma domin ingiza jama'a a kan gwamnatin Buhari. Halin da Sanatan ya ce ba na dattijai ba ne.
Sanata Adamu ya shawarci Sanatocin da su bayyana ra'ayi ko bayar da shawara ba tare da amfani da kalamai masu kaushi ba.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng