Dazunnan: Atiku Abubakar, ya taya Obasanjo, ogansa a da, murnar gama makarantar jami'a

Dazunnan: Atiku Abubakar, ya taya Obasanjo, ogansa a da, murnar gama makarantar jami'a

- A shafinsa na Tuwita @Atiku, ya taya tsohon ogansa murnar zama Dakta

- Obasanjo ya koma makaranta shekaru 10 da suka wuce

- An sha samun takun-saqa da abokan junan kan kujerar mulki a da

Dazunnan: Atiku Abubakar, ya taya Obasanjo, ogansa a da, murnar gama makarantar jami'a
Dazunnan: Atiku Abubakar, ya taya Obasanjo, ogansa a da, murnar gama makarantar jami'a

Atiku Abubakar, tsohon mataimaki ga Olusegun Obasanjo, ya amsa kuwwar masu taya tsohon ogan nasa murnar hada digiri na ukku, wato doctorate, bayan da Obasanjon ya hattama karatun nasa cikin shekaru 11.

A shafinsa na tuwita, dazunnan da rana, Atikun yace: 'Komawarka makaranta, a shekarunka na dattijo, ya koyarwa da 'yan baya cewa ilimi ba'a yi masa girma, ina taya ka murna Oga'.

DUBA WANNAN: 'Yar tsana domin soyayyar marasa budurwa a N700,000

Sun dai daro siyasarsu tare tun tali-tali, kamar shekaru 25 da suka wuce, kuma sun mulki kasar nan tare a 1999-2007, sai dai sun bata da juna saboda neman tazarce da neman kujerar ga dukkansu jerau.

A yanzu dai komawar Atikun PDP na nuna yana sake sansanar kujerar ta Ogansa wadda ke hannun Buharin APC, kuma ana sa rai zai nemi sahalewar Obasanjon, dattijo a kasa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng