Karin jihohi a kasar nan: Wai zancen ya kwana da majalisar dattijai tayi alkwari?
Tun 1996, zamanin mulkin soji, ba'a sake karin jihohi a kasar nan ba, shekaru 22 da suka wuce kenan, sai dai bayan samuwar jamhuriya ta shidda, sai aka fara kiraye-kirayen a sake kara jihohi, inda yankuna da dama ke son a basu 'yanci daga wasu kabilun a jihohinsu
Tun 1996, zamanin mulkin soji, ba'a sake karin jihohi a kasar nan ba, shekaru 22 da suka wuce kenan, sai dai bayan samuwar jamhuriya ta shidda, sai aka fara kiraye-kirayen a sake kara jihohi, inda yankuna da dama ke son a basu 'yanci daga wasu kabilun a jihohinsu.
Majalisar dattijai dai ita ce take wannan aiki kafin zabukan 2015, amma kuma, tun bayan hawan jam'iyyar APC sai aka ji shiru, kan batun, bada ma karin jihohi, ko taron kasa da aka yi a 2014, aka kashe wa wakilai kudade, APC ta wullar a kwandon shara.
DUBA WANNAN: Kanawa na fargabar za'a zub da jini a 30 ga Janairu
Yanzu dai shiru kake ji, babu ko batun karin jihohin, duk da alkawurra da a baya 'yan siyasa suka sha dauka.
Sai zabe ya zo sannan za'a sake jin duriyar batun sake kirkirar jihohi, ga kowanne yanki da suke son kafa sabuwar jiharsu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng