Karya ta kare: An cafke wasu 'yan kungiyar asiri suna tsaka da gudanar da taro da talatainin dare
- An cafke 'yan kungiyar asiri yayin da suke tsaka da gudanar da taro da talatainin dare
- An cafke 'yan kungiyar asirin ne a jihar Legas
- Jami'an hukumar tsaro mai yaki da aiyukan ta'addanci a jihar Legas (LNSC) ce ta yi nasarar cafke 'yan kungiyar asirin
Jami'an hukumar tsaro mai yaki da aiyukan ta'addanci a jihar Legas (LNSC) ta yi nasarar cafke wasu 'yan kungiyar asiri yayin da suke tsaka da gudanar da taro da talatainin dare a unguwar Eputu dake karkashin karamar hukumar Ijebu-Lekki dake jihar Legas.

Shugaban hukumar LNSC, Mista Lateef S. O., ya ce ya bayyana cewar 'yan kungiyar asirin sun dade suna aikata miyagun laifuka a yankin na Ijebu-Lekki, tare da bayar da tabbacin cewar, nan bada dadewa ba ragowar abokan 'yan kungiyar za su shigo hannun hukumar.
DUBA WANNAN: Matasa miliyan daya zasu samu rancen kudi daga bilyan N10 da gwamati ta ware karkashin sabon shirin NEPRO
Kazalika, shugaban karamar hukumar, Ijebu-Lekki, Honarabul Dakta Kemi Surakat, ya gane ma idanunsa 'yan ta'adan kafin a wuce shelkwatar hukumar LNSC ta jihar Legas.
Dakta Surakat ya ce gwamnatin jihar Legas ba za ta bar 'yan ta'adda su ci karensu babu babbaka ba a jihar. Sannan ya kara jaddada aniyar gwamnatinsa na kare rayuka da dukiyoyin jama'ar karamar hukumar Ijebu-Lekki.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng