Dubi hotunan amarya yayin da ta Haukace ana tsaka da shagalin bikinta, har ma ta yayyaga kayan amarcinta

Dubi hotunan amarya yayin da ta Haukace ana tsaka da shagalin bikinta, har ma ta yayyaga kayan amarcinta

- Amarya ta haukace ana tsaka da shagalin bikinta

- Ta yayyaga kayan amarcinta

- Ana zargin kishiyar uwarta da yi mata asiri

A ranar da ya kamata ta kasance mata ranar farinciki da alfahari, sai ga shi wata kyakykyawar amarya ta haukace ana tsaka da shagalin bikinta.

Dubi hotunan amarya yayin da ta Haukace ana tsaka da shagalin bikinta, har ma yayyaga kayan amarcinta
Amarya yayin da ta Haukace ana tsaka da shagalin bikinta

Wani shaidar gani da ido ya ce amaryar ta fara haukan ne yayin da suke tsaka da taka rawa ita da angonta. Ya ce amaryar ta fara da cire gyauton da take sanye da shi kafin daga bisani ta fara yayyage kayan dake jikinta.

DUBA WANNAN: Zaman lafiya ya samu: Hotuna masu kayatarwa daga wani bikin nishadi da aka gudanar a Maiduguri

Duk da ya zuwa yanzu ba'a tantance da mene ne ya haddasa haukacewar amaryar ba, 'yan uwanta sun dora laifin abinda ya samu amaryar a kan kishiyar uwarta, wacce suka ce bata son ganin amaryar ta yi aure.

Wannan abin tausayi ya faru ne a garin Masaka dake kasar Uganda.

Saidai rahoton da muka samu bai ambaci sunan amaryar ko angonta ba, saidai jama,a a dandalin sada zumunta sun cigaba da tofa albarkacin bakinsu a kan faruwar al,amarin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng