LABARI DA DUMI-DUMI: An yi garkuwa da 'yan uwan mata uku a Neja

LABARI DA DUMI-DUMI: An yi garkuwa da 'yan uwan mata uku a Neja

- Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da 'yan uwan mata uku a Neja

- Masu garkuwa da mutanen sun sace 'yan matan ne a safiyar ranar Asabar a garin Kuchi da ke jihar Neja

- ‘Yan bindigar da kansu suka kira shugaban karamar hukumar Munya kuma suka sanar da shi cewa sun sace 'yan uwansa

Wasu ‘yan bindiga da ba a tantance ba sun yi awon gaba da wasu ‘yan uwan mata uku na shugaban karamar hukumar Munya da ke jihar Neja.

An ce masu garkuwa da mutanen sun sace 'yan matan ne a safiyar ranar Asabar, 20 ga watan Janairu a gidan shugaban a garin Kuchi.

Shaidu sun bayyana cewa 'yan bindigar sun yi ta harbi a iska don hana mutane su zo don ceton ‘yan matan.

Minna: An yi garkuwa da 'yan uwan mata uku a Nejar

‘Yan bindiga masu garkuwa da mutane

Rahotanni sun nuna cewa ‘yan bindigar sun kira shugaban kuma suka sanar da shi cewa sun sace 'yan uwansa ba tare da sunyi ko kuma suna neman wani fansa ba.

KU KARANTA: Rashin Imani: Ya sayar da yaron mutane kan N70,000

A cewar rahotanni, masu sace-sacen suna amfani da gandun dajin Kabula da sauran dajin da ke makwabta don su ɓoye wadanda suka sace daga yankin.

A halin yanzu, kwamishinan 'yan sandan jihar Neja, ta hanyar kakakinsa, Mohammed Abubakar, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce ‘yan sanda suna kokarin ceton 'yan matan da kuma kama wadanda suka sace su.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel