Sanatan da ya kai budurwarsa kara kotu kan N750,000 da ya kashe mata bisa soyayya

Sanatan da ya kai budurwarsa kara kotu kan N750,000 da ya kashe mata bisa soyayya

- Sanatan ya fito daga kasar Kwara ne, ya kuma taba neman gwamna a jam'iyyar AD

- Ya ce ya kashe kudin ne a kan karatunta, domin haka ya je kotu

- Ta ki aurarsa ne bayan da ya gama bautar ta samari

Sanatan da ya kai budurwarsa kara kotu kan N750,000 da ya kashe mata bisa soyayya
Sanatan da ya kai budurwarsa kara kotu kan N750,000 da ya kashe mata bisa soyayya

Bayan kashe mata kudade da suka kai kusan miliyan daya na nairori, Sanata daga Kwara, kuma tsohon mai takarar Gwamna a AD, Suleiman Makonjuola, ta shiggar da kara a kotun jiharsa, inda yake nema masoyiyarsa (ba ita ce a hoton sama ba), ta biya shi kudin da ya kashe mata na karatu.

Halimat Temitokpe Abdulaziz, ta ci kudin Sanatan ne da sunan soyayya, kuma wai da alkawarin aure, sai dai yanzu da ta gama karatu, tace ita kam, ta yafe aure da shi, abin da ya bakantawa jarumin masoyin rai/

DUBA WANNAN: Yar tsanar roba don saduwa ta kawo tarnaqi a al'umma

A cewar lauyan sanatan, dama rance ta nema na rabin miliyan, kafin babanta ya samu a biya shi albashinsa, kuma ya bata, shine ma kuma ya sama mata admission din makarantar ta KWASU, wato jami'ar jihar.

A cewarsa a Whatsapp ne suka hadu, kuma sun dana soyayya inda take zuwa har gidansa. Sai dai bayan da ya zo da magganar aure, sai ta ce fau-fau, inda ta kaurace masa na kusan wata daya, lamarin da ya sanya shi neman bahasi, da ma kokarin dawo da kudinsa.

Sanatan ya kuma ce ta sake arar kudi N200,000 domin ta taimakawa iyayenta, wanda hakan ma ya kara musu dankon soyayya a lokacin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng