Wutar dare ta kone gidaje 3 da dukiyoyin miliyoyin Nairori a wannan jihar

Wutar dare ta kone gidaje 3 da dukiyoyin miliyoyin Nairori a wannan jihar

Labarin da muke samu daga majiyoyin mu na nuni ne da cewa wutar dare a jiya juma'a ta kone gidaje manya-manya guda uku tare kuma da dukiyoyin miliyoyin Nairori a rukunin gidaje na Gowon mallakin gwamnatin tarayya a jihar Legas.

Majiyar mu dai ta tabbatar mana da cewa ba'a samu asarar rayuka ba sakamakon wutar.

Legit.ng ta samu haka zalika cewa wasu da lamarin ya auku a kan idon su sun tabbatar da cewa wutar ta soma ci ne da misalin karfe 7:15 na yamma a daya daga cikin gidajen kafin daga bisani ta watsu zuwa sauran gidajen.

Wutar dare ta kone gidaje 3 da dukiyoyin miliyoyin Nairori a wannan jihar

Wutar dare ta kone gidaje 3 da dukiyoyin miliyoyin Nairori a wannan jihar

A wani labarin kuma, mun samu cewa Jami'an rundunar hukumar 'yan sandan kasar Najeriya shiyyar jihar Taraba ta sanar da ladar makudan kudin da suka kai Naira 10 miliyan ga duk wanda ya bayyana masu wani bayanin da zai taimaka wajen damke bata-garin da suka kashe dan majalisar Taraba, Mista Hosea Ibi.

Kwamishinan 'yan sandan jihari mai suna Mista Dave Akinremi shine ya sanar da hakan a yayin da yake zantawa da manema labarai jiya Juma'a a garin Jalingo babban birnin jihar.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel