Jerin sunayen hukumomin tsaro a Najeriya, da ayyukansu
- Tsaro sai da shi ne yake hana a kwace maka kudi a aljihu
- Idan babu tsaro ko mai kanti zai rasa kayansa ba abinda zayyi
- Duk da matsalar tsaro, har yanzu dai akwai doka da oda a kasa fiye da wasu kasashen
A lissafi akwai kafaffen tsaro da yawa a Najeriya, kowanne da aikinsa da doka ta tadanar masa, ga su a jere:
1. Sojoji: Akwai Nigerian Army, Airforce da Navy, na kasa da na sama da na ruwa, aikinsu kuma shine kare iyakokin Najeriya daga kutse.
2. 'Yansanda: Aikinsu tsare doka da Oda a cikin gida
3. SSS ko DSS: Aikinsu leken asiri a cikin gida, da tsaro
4. NIA: Sune masu leken asiri a kasashen waje domin moriyar gida
5. EFCC: Binciken kudaden sata
DUBA WANNAN: Yadda Buhari yayi fatali da rahoton Kingibe a NIA
6. NDLEA: Masu kama kwayoyi
7. FRSC: Masu kare titunan kasa
8. Customs: Masu kama kayan fasa kwabri
9. Immigration: Masu duba su waye ke shige da fice a kasa
10. Civil Defence: Aikinsu kare kadarorin kasa daga tu'annati
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng